Bangaren jam’iyyar PDP da Kabiru Turaki ke jagoranta ya bayyana cewa kotun ƙolin Najeriya ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa INEC ba ta da hurumin ƙarshe a kan lamarin. Sun ce sun riga sun garzaya kotun domin neman hukunci na ƙarshe.

Wannan na zuwa ne bayan INEC ta amince da shugabancin bangaren da ke goyon bayan Nyesom Wike, inda ta sanya sunan Abdulrahman Mohammed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa bayan wani taro da aka gudanar a Abuja. Sai dai bangaren Turaki ya ƙi amincewa da taron, yana mai cewa an yi shi ba bisa ƙa’ida ba yayin da shari’a ke gudana.

Bangaren ya kuma zargi gwamnatin Bola Tinubu da hannu a rikicin cikin gida na PDP, yana mai cewa ana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa. A cewarsu, rikicin na ƙara tsananta yayin da kowanne bangare ke neman iko a jam’iyyar, lamarin da ke ci gaba da kasancewa a gaban kotu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version