An kashe fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Sani Yellow, a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara. Sai dai rahotanni sun bambanta kan yadda lamarin ya faru, inda wasu suka ce wasu ‘yan bindiga masu biyayya ga Dogo Gide ne suka harbe shi a kasuwar Dan Jibga, yayin da wasu majiyoyin tsaro suka ce an kashe shi ne a wani samame da jami’an tsaro suka gudanar tare da ‘yan sa-kai na Maiduguri Special Vigilantes.
Majiyoyin tsaro sun ce samamen na daga cikin hare-haren da ake kai wa maboyar masu aikata laifuka da manyan jagororin ‘yan bindiga a Zamfara. Duk da haka, har zuwa lokacin fitar da rahoton, hukumomin tsaro ba su tabbatar da ainihin yadda Sani Yellow ya mutu ba.
A halin da ake ciki, rahotanni sun ce an kai sabbin hare-hare a karamar hukumar Tsafe, inda ake zargin mabiyan Adamu Aliero da kashe akalla mutum biyu tare da sace sama da mutum 60. An kuma ce maharan sun kwashe kayan abinci da dabbobi, yayin da dakarun Operation FANSAN YANMA suka ƙara sintiri tare da fara farautar maharan domin ceto waɗanda aka sace da hana sake aukuwar hare-hare.
