Wasu matasa da ɗalibai a jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da matsalar rashin tsaro, tare da kira ga ‘yan Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da sauran ayyukan laifi. An gudanar da gangamin ne a Maiduguri ƙarƙashin taken #UniteAgainstTerror.
Jagoran Ƙungiyar Matasa da Ɗalibai ta Borno, Suleiman Muhammed, ya yabawa gwamnatin tarayya kan ceto ɗaliban da aka sace a jihar Oyo, tare da buƙatar ta ƙara ƙaimi wajen ceto sauran waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane a Borno. Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su biya kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda.
Masu zanga-zangar sun kuma buƙaci gwamnati ta ƙara saka hannun jari a fannin tsaro, ta inganta walwalar jami’an tsaro, tare da samar wa matasa ayyukan yi da yanayi mai kyau na rayuwa domin rage aikata laifuffuka da kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.
