Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da ke ƙarfafa tattalin arzikin jihar tare da inganta ayyukan gwamnati. Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi ta Ƙasa (RMAFC) a gidan gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce ingantattun gyare-gyare, amfani da fasaha da ƙarfafa gaskiya sun taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR). Ya ce ƙaddamar da shirin Project C.R.A.F.T. da dandalin PAYKADUNA sun sauƙaƙa biyan kuɗaɗen shiga tare da rage asarar kuɗaɗe da ƙara amincewar jama’a ga gwamnati.

Uba Sani ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta bunƙasa fannin lafiya da ilimi, inda aka inganta cibiyar lafiya guda a kowace ƙaramar hukuma tare da samar da kayan aikin zamani da motocin daukar marasa lafiya. Haka kuma ya ce yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu daga kimanin 535,000 a shekarar 2023 zuwa 187,720, yayin da aka ware kashi 26.5 na kasafin kuɗin jihar domin ilimi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version