Wani gagarumin lamari ya faru a Fadar Gwamnatin Kano da safiyar Litinin, inda wani barawo ya kutsa cikin harabar gidan gwamnati ba tare da izini ba, ya kuma sace wata mota kirar Toyota Hilux daga cikin jerin motocin mataimakin gwamna. Lamarin ya faru ne ba tare da jami’an tsaro sun lura da shi ba, abin da ya tayar da hankali tare da nuna gibin tsaro a cikin fadar.

Rahotanni daga cikin fadar sun bayyana cewa bayan duba faifan bidiyon CCTV, an gano cewa wanda ya aikata laifin ya shiga ta ƙofa mai lamba 4 sannan ya fita ta babban ƙofar gidan gwamnati cikin natsuwa. Majiyoyi sun ce ofishin mataimakin gwamnan ba ya samun tsaron dindindin sai a lokacin aiki, wanda hakan na iya zama dalilin da yasa lamarin ya gudana cikin sauƙi.

Direban motar da aka sace, wanda aka bayyana da suna Shafiu Sharp-Sharp, an tsare shi domin bincike yayin da Babban Jami’in Tsaro ke nazarin bidiyon don gano barawon. Hukumomin tsaro sun riga sun baza bayanan motar ga sauran sassa na tsaro a fadin ƙasa domin a kamo wanda ya aikata wannan laifi mai nuna raunin tsaro a Fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version