Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood, Alhaji Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Na Ta’ala daga shirin “Dadin Kowa” na Arewa24, ya rasu bayan doguwar jinyar ciwon daji (cancer) ya yi fama da shi. Marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri a ranar Lahadi, 2 ga Nuwamba, 2025.
An gudanar da sallar jana’izarsa a masallacin Juma’a na Sarkin Fika da ke Potiskum, Jihar Yobe, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a ranar Litinin, inda aka binne shi a garin nasa. An haifi marigayin a Potiskum ranar 15 ga Agusta, 1967, kuma ya fara wasan kwaikwayo tun a shekarar 1982. Ya yi fice a cikin fina-finai masu barkwanci tare da fitattun jarumai kamar marigayi Rabilu Musa (Dan Ibro), kafin shirin Dadin Kowa ya karrama shi da suna Malam Na Ta’ala.
Baya ga wasan Dadin Kowa, Malam Na Ta’ala ya taka muhimmiyar rawa a fim ɗin “A Duniya”, inda ya fito a matsayin malamin makarantar allo. A watannin baya ne aka bayyana cewa yana fama da cutar daji, inda ya roƙi tallafi daga jama’a don biyan kuɗin magani da jinya da ke kaiwa N250,000 kowane mako uku.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 58, ya bar mata uku da ’ya’ya goma. Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya taimaka masa wajen kula da lafiyarsa, tare da wasu ’yan siyasa da abokan harkar fina-finai. Haka kuma, shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdulrahman Tchani, ya taimaka masa da gudummawar da ta taɓa zukatan jama’a.
