Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi zargin cewa jami’an hukumar shige da fice sun hana ta fita ƙasar waje a filin jirgin sama, inda suka kwace mata fasfo ɗinta ba tare da wani dalili na doka ba. A wani faifan bidiyo da ta yada kai tsaye a Facebook, Sanatar ta bayyana cewa hakan ya saba mata haƙƙin tafiya da na ’yancin ta a matsayinta na ƴar ƙasa, tana mai cewa an taba yi mata irin wannan cin zarafi a baya.

Natasha ta ce jami’an sun shaida mata cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayar da umarnin a hana ta fita daga ƙasar, bisa zargin cewa tana “ɓata sunan ƙasa” a kafafen yada labarai na ƙasashen waje duk lokacin da ta yi tafiya. Ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira “cin mutunci da tsangwama daga masu iko,” tana roƙon gwamnati ta kawo ƙarshen abin da ta ce na zama barazana ga mata masu tsayawa da gaskiya a siyasa.

Sai dai hukumar shige da fice ta ƙaryata wannan zargi, inda kakakinta, Akinsola Akinlabi, ya bayyana lamarin a matsayin “binciken yau da kullum” da ya ɗauki ’yan mintuna kaɗan kafin a sake mata fasfo ɗinta. Akinlabi ya ce babu wata alaƙa tsakanin hukumar da majalisar dattawa a wannan lamari. Duk kokarin da aka yi domin samun karin bayani daga ofishin Akpabio bai yi nasara ba, domin bai ɗaga waya ko amsa saƙo ba.

Lamarin ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman ganin cewa Natasha ta dade tana rikici da shugabancin majalisar tun bayan dakatar da ita a watan Maris 2025, sakamakon zargin ta da cewa Akpabio yana tafiyar da majalisar “ta zalunci.” Duk da cewa an dawo da ita ofis a watan Satumba, wannan sabon rikicin ya sake hura wutar muhawara kan dangantakarta da shugabancin majalisar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version