Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa babu ja da baya kan fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga Janairu, kamar yadda aka tsara. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce an bi dukkan ka’idojin doka tun daga tattaunawa da masu ruwa da tsaki, amincewar Majalisar Tarayya, har zuwa rattaba hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa akwai nau’i guda ɗaya kacal na dokokin harajin da aka amince da su kuma Shugaban Ƙasa ya sanya hannu a kai.
Dangane da korafe-korafen da ke yawo cewa an sauya wasu sassa na dokar bayan an fitar da ita a jarida ta hukuma, Idris ya ce batun yana hannun Majalisar Tarayya, wadda ta kafa kwamitin bincike don tantance gaskiyar lamarin. Shi ma Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya gargadi jama’a da kada su yanke hukunci bisa takardun da ba su da sahihanci, yana mai cewa nau’in dokar da ke da ƙarfi shi ne wanda Majalisa ta tabbatar kuma ta miƙa wa Shugaban Ƙasa.
Tsohon Shugaban Hukumar FIRS, Muhammad Nami, ya ce ya kamata a yi bincike mai zurfi maimakon a yi kira da a janye dokokin gaba ɗaya. Ya jaddada cewa sabbin dokokin an tsara su ne domin toshe ɓarayin kuɗaɗen haraji, ƙara kuɗaɗen shiga, tallafa wa ci gaban tattalin arziƙi, da samar da manyan ayyukan more rayuwa. A cewarsa, idan aka aiwatar da dokokin yadda ya kamata, za su taimaka wajen sauƙaƙa biyan haraji da ƙarfafa gwiwar masu zuba jari a Najeriya.
