Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi gargadi cewa jam’iyyar PDP na iya fuskantar koma baya a babban zaɓen 2027 idan shugabancinta ya gaza magance rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar. Wike ya bayyana wannan matsayi ne a ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers.
A jawabin nasa, Wike ya bukaci shugabannin PDP su ɗauki matakan gaggawa wajen warware rikicin kafin a shiga zagayen zaɓen gaba. Ya yi nuni da cewa shugabancin jam’iyyar ba ya nuna cikakken mayar da hankali ga matsalolin da ke addabar PDP kuma bai karɓi shawarwari ba.
Ya ƙara da cewa, “Idan shugabanni jam’iyyar suka amince da sun yi kuskure tare da tambayar kansu abin da ke haddasa matsalolin da suka fuskanta da kuma yadda za a gyara su, to jam’iyyar za ta iya farfadowa.”
Tun bayan zaɓen 2023, PDP ta sha fama da rikice-rikice cikin gida, lamarin da ya jawo ficewar wasu mambobinta ciki har da gwamnoni masu ci zuwa jam’iyyar APC.
