Gahugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya musanta cewa binciken da ake wa tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami, yana da alaƙa da barinsa jam’iyyar APC. A wata hira da gidan talabijin Channels, Olukoyede ya ce binciken ya fara tun kafin ya karbi shugabancin hukumar, kuma abin da ya yi shi ne tabbatar da gudanar da binciken cikin tsari da inganci.
Olukoyede ya nanata cewa ci gaban Najeriya ba zai yiwu ba idan ana ɗaukar bincike da bambancin siyasa. Ya ce yaƙin cin hanci da rashawa da EFCC ke yi ya zama aikin hukuma kawai, kuma dole ne ‘yan Najeriya su amince cewa hukumar na aiki ba tare da nuna ɓangare ba.
Hukumar ta gudanar da binciken Malami na kusan shekaru biyu da rabi kan zargin halasta kuɗaɗen haramun, wanda ya kai ga tsare shi da iyalansa a gidan yarin Kuje, Abuja. Daga baya kotu ta bayar da belinsu kan kuɗi naira miliyan 500 tare da kawo mutum biyu a matsayin waɗanda za su tsaya musu.


