Fitaccen shugaban ‘yan bindiga Bello Turji ya musanta zargin karɓar kuɗi ko motoci daga gwamnatin Jihar Zamfara, yana mai cewa tun daga haihuwarsa bai taɓa mallakar N5m ba. Turji ya faɗi hakan ne a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, domin martani ga zargin da tsohon mai sasanci, Musa Kamarawa, ya yi masa.
Kamarawa ya yi ikirarin cewa Turji ya karɓi N30m da kuma motoci a lokutan tattaunawar sulhu da tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, amma Turji ya ƙaryata hakan gaba ɗaya. Ya zargi Kamarawa da cin amana da yaɗa ƙarya, yana mai cewa ba don riba yake aikata abin da yake yi ba, kuma ba shi da alaƙa da kowanne ɗan siyasa ko ƙungiya ta siyasa.
Turji ya kuma dora alhakin tabarbarewar tsaro kan wasu tsofaffin shugabanni, yana kiran a bincike su, yayin da mazauna Sokoto da masu fafutukar kare haƙƙin jama’a suka yi gargaɗin cewa ana siyasantar da matsalar tsaro gabanin zaɓen 2027. Duk da ikirarin nasa, jami’an tsaro sun tabbatar da cewa Turji na daga cikin manyan ‘yan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Arewa maso Yamma.
