Hukumar Nigerian Safety Investigation Bureau (NSIB) ta fara bincike bayan wani jirgin Hawker 800XP ya fuskanci matsala a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda mutane takwas da ke cikinsa suka tsira ba tare da jin rauni ba. Lamarin ya faru ne Lahadi, 14 ga Disamba, 2025, yayin da jirgin ya taso daga Abuja zuwa Kano, kuma ya sauka da misalin ƙarfe 10:34 na safe.

NSIB ta bayyana cewa jirgin, mallakin Flybird Aircraft Management Services Limited, ya samu matsalar alamar na’urar tayar sauka (landing gear) tun kafin saukowa, lamarin da ya sa matukan jirgin suka yi zagaye sau da dama domin jami’an kula da zirga-zirgar jirage su tabbatar da matsayin tayoyin. Duk da an tabbatar da cewa tayoyin sun fito yadda ya kamata, sai dai bayan sauka tayoyin gaba sun rushe yayin da jirgin ke rage gudu a kan titin sauka.

NSIB ta jaddada cewa binciken ba wai don dora laifi ba ne, sai dai domin gano matsalolin tsaro da hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba. Kamfanin Flybird ya kuma tabbatar da cewa an bi dukkan ka’idojin tsaro, kuma duk fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun sauka lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version