Aƙalla mata da yara kusan 100 ne aka sace bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari wani sansanin ‘yan gudun hijira a Borno State da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun ce an kashe sojoji tara a harin da aka kai garin Ngoshe, yayin da maharan suka cinnawa motoci da tankokin mai wuta tare da kwashe makamai masu yawa.

Har ila yau maharan sun kashe limamin masallacin sansanin ‘yan gudun hijirar kafin su yi awon gaba da mata da yara. Wani ɗan majalisar yankin ya bukaci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi domin daƙile hare-haren Boko Haram a yankin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version