Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sallami dakatararren mataimakin kwamishinan ‘yansanda, Abba Kyari, tare da wanke shi daga zarge-zargen da ake masa na rashin bayyana kadarorinsa.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin kan tuhume-tuhume guda 23 da hukumar National Drug Law Enforcement Agency ta shigar a kansa, inda ta zarge shi da kin bayyana wasu kadarori.

TVC News ta rawaito cewa an gurfanar da Kyari tare da wasu ‘yan’uwansa biyu da ake zargin sun yi rantsuwar ƙarya domin ɓoye asalin mamallakin wasu dukiyoyi, amma kotun ta ce NDLEA ta kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin. Alƙalin ya kuma bayyana cewa ana iya mallakar fili ta hanyoyi daban-daban kamar gado ko kyauta.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version