Gwamnatin kasar China ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai gargadin Amurka da kada ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan abin da ya kira kisan Kiristoci, inda ya bayyana Najeriya a matsayin “Kasa mai damuwa ta musamman” tare da yin barazanar katse tallafi da ma daukar matakin soja.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ta bayyana cewa Najeriya abokiyar hulda ce ta dabarun ci gaba ga kasar Sin, kuma Beijing tana adawa da duk wata kasa da ke amfani da batutuwan addini ko hakkin dan Adam wajen tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe. Ta ce China na marawa Najeriya baya wajen tafiyar da harkokinta bisa tsarin da ya dace da bukatunta da yanayinta.
Masana harkokin kasa da kasa sun ce wannan rikici na nuna yadda Amurka ke damuwa da karuwar tasirin China a Najeriya da sauran kasashen Afrika. Rahotanni sun bayyana cewa hadin kai tsakanin Abuja da Beijing yana kara karfafa gasa tsakanin manyan kasashen duniya kan tasiri a nahiyar Afrika.
