Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa jihar ta soma cin moriyar cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta aiwatar. Gwamnan ya ce matakin, duk da cewa ya kasance bai yi wa jama’a dadi ba a farko, amma yana daga cikin gyare-gyaren da suka ceci Najeriya daga durkushewa, tare da samar da karin kudaden shiga ga jihohi.

Yahaya ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da takardun biyan tsoffin ma’aikata na fansho da hakkokinsu a Gombe. Ya ce karin kudaden da jihohi ke samu daga Abuja sakamakon cire tallafin mai ya bai wa gwamnati damar gudanar da manyan ayyukan raya kasa da ba za su yiwu ba a da.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ware N8.2 biliyan domin biyan bashin tsoffin ma’aikata sama da 3,000 na jihar da kananan hukumomi. Ya ce daga cikin kudin, N6.6 biliyan za a biya ma’aikatan gwamnatin jiha, yayin da N1.6 biliyan za su tafi ga ma’aikatan kananan hukumomi.

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu, gwamnatin sa ta riga ta biya bashin fansho da ya kai N33.8 biliyan — adadi mafi girma a tarihin jihar. Ya jaddada cewa wannan ne karon farko da gwamnati ta nuna irin wannan jajircewa wajen kula da walwalar tsoffin ma’aikata da suka ba da gudunmawa wajen gina jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version