Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, bayan ya karɓi ragamar aiki daga hannun CP Ajao Adewale a ranar Juma’a, 17 ga Oktoba, 2025. Nadinsa ya biyo bayan sauyin wurin aiki da Babban Sufeton ’Yan Sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya gudanar.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana kudirinsa na inganta tsaro da ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummar Abuja. Ya ce zai samar da tsare-tsare masu inganci don kare rayuka da dukiyoyin mazauna Babban Birnin Tarayya tare da neman goyon bayan jama’a wajen tabbatar da zaman lafiya.

Dantawaye Miller, wanda aka haifa a Kajuru, Jihar Kaduna a ranar 15 ga Oktoba, 1971, ya shafe fiye da shekaru 20 a rundunar ’yan sanda, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a jihohi da hukumomi na tarayya. Ya fara aikin ’yan sanda a 2000 kuma ya yi aiki a Bayelsa, Yobe, Edo, Adamawa da Abuja, gami da zama kwamandan MOPOL 24 a Fadar Shugaban Ƙasa da kwamishinan fasahar sadarwa a hedikwatar rundunar. Kafin wannan mukami, shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi.

Nadinsa na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Birnin Tarayya ke fuskantar ƙarin ƙalubalen tsaro. Ana sa ran gogewarsa da sabbin dabarunsa za su taimaka wajen ƙarfafa matakan tsaro da kawo sauyi a ayyukan ’yan sanda a Abuja.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version