Jami’an DSS sun kama mutum na shida da ake zargi da hannu a harin cocin Katolika na St. Francis Catholic Church Owo a shekarar 2022. Harin ya kashe fiye da masu ibada 40 tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda NTA ta ruwaito.

Wanda aka kama, mai suna Sani Yusuf, ya shafe kusan shekara huɗu yana ɓuya kafin a cafke shi a Iguosa da ke jihar Edo. Majiyar tsaro ta ce shi babban kwamanda ne a ISWAP, kuma bayan harin ya tsere zuwa Kano kafin daga bisani ya koma ɓuya.

Rahotanni sun ce ya amsa hannu a harin cocin da kuma wasu hare-hare, ciki har da farmaki a barikin sojoji na Suleja da sace-sace a Kaduna da kewaye. Haka kuma ya amince da hannu a harin shingen sojoji na Zuma Rock, yana mai cewa ya taɓa aiki ƙarƙashin jagora mai suna Abu Ikirimah.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version