Dukkan ’yan majalisar wakilai na jihar Enugu da ke majalisar tarayya sun sauya sheka daga jam’iyyun PDP da Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC). Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya shekar a zaman majalisar da aka yi a ranar Alhamis 30 ga Oktoba, inda Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya halarci taron a matsayin shaida.

A lokacin da yake magana da manema labarai, dan majalisar da ke wakiltar Nkanu East/Nkanu West, Nnolim Nnaji, ya bayyana cewa matakin nasu ya samo asali ne daga bukatar hada kai da gwamnatin Mbah da ke gudanar da ayyukan ci gaba a jihar. Ya ce lokaci ya yi da Enugu za ta shiga cikin tsarin mulkin kasar domin samun ci gaba da ayyukan raya kasa.

Nnaji ya kara da cewa wannan sauyi ba kawai siyasa ba ce, amma “mataki ne na tsantsar hangen nesa da jajircewa domin daukaka al’ummar Enugu.” Ya ce shiga APC zai taimaka wajen kawo ayyuka, inganta hanyoyi, samar da guraben aiki, da karfafa matasa da mata a yankin.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai Martins Oke, Anayo Onwuegbu, Nnamdi Agbo, Nnolim Nnaji, da Mark Obetta. Haka kuma, dan majalisar da ke wakiltar Bassa/Jos North, Daniel Asama, ya bar Labour Party ya koma APC. Wannan sauyi ya baiwa APC cikakken rinjaye kan dukkan ’yan majalisar wakilai daga jihar Enugu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version