Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ministan Albarkatun Man Fetur, Chief Timipre Sylva, a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo, bisa zargin hada baki da karkatar da dala miliyan $14.8. EFCC ta ce kudaden sun fito ne daga tallafin da Hukumar Kula da Cigaban Albarkatun Man Najeriya (NCDMB) ta saka a aikin gina masana’antar tace mai a Brass, cikin Bayelsa, wanda kamfanin Atlantic International Refinery ke jagoranta.

Rahotanni sun nuna cewa an zuba dala miliyan $35 a aikin tun 2020 don gina masana’antar mai mai iya tace ganga 2,000 a rana tare da wasu kayayyaki kamar tashar jiragen ruwa da wutar lantarki, amma har yanzu aikin ya tsaya cak babu wani ci gaba da za a gani. EFCC ta riga ta kama da kuma gudanar da bincike kan shugabannin wasu daga cikin masu gudanar da aikin, ciki har da tsohon sakataren NCDMB da kuma shugaban kamfanin da ya jagoranci shirin.

Sai dai Sylva ta bakin mai magana da yawunsa, Julius Bokoru, ya karyata zargin, yana cewa wannan mataki wani sabon yunkuri ne na bata masa suna ta siyasa. Ya ce EFCC ba ta kira ko sanar da shi kafin fitar da sanarwar neman sa ba, kuma hakan ya nuna an shirya lamarin ne domin tada jijiyoyin wuya da tunzura jama’a. Ya kara da cewa Sylva yanzu yana kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Tawagar Sylva ta ce za shi girmama duk wata gayyata daga hukumar idan aka turo ta yadda ya dace, tare da jaddada cewa aikin gina matatar mai yana da cikakken takardu da tsarin aiki. Sun roki magoya baya su kwantar da hankula, suna mai cewa gaskiya za ta bayyana daga karshe, duk wani yunkuri na rage tasirin siyasar Sylva ba zai yi nasara ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version