Hukumar EFCC ta tabbatar da tsare tsohon Ministan Ƙwadago kuma tsohon Gwamnan Anambra, Chris Ngige, bayan yaɗuwar jita-jitar cewa an sace shi. Mai magana da yawunsa, Fred Chukwuelobe, ya bayyana cewa Ngige yana hannun EFCC ne cikin koshin lafiya.

Chukwuelobe ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa tsohon ministan bai samu matsala ta sacewa ba, sai dai hukumar ta kira shi don wani bincike da ba a bayyana ba tukuna. Wannan ya kawo ƙarshen cece-kuce da ya taso bayan rahotannin farko da suka yaɗu.

EFCC har yanzu ba ta fitar da cikakkiyar sanarwa kan dalilin tsare Ngige ba, amma ana sa ran hukumar za ta yi bayani a hukumance kan irin binciken da ake gudanarwa a kansa. Lamarin ya jawo hankalin jama’a ganin cewa shi ne na biyu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Buhari da ake tsarewa a makonnin nan.

Kafin Ngige, an tsare tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda har yanzu yake hannun hukumar domin amsa tambayoyi kan wasu zarge-zarge da ake masa. Wannan sabon mataki na EFCC ya sake haifar da tattaunawa game da kamfen ɗin yaki da cin hanci a Najeriya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version