Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda ake amfani da jami’an tsaro wajen kare wasu manyan ‘ya’yan gwamnati, musamman Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa. Ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin bayar da lambar yabo ta Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism da aka gudanar a Legas.

Soyinka ya ce abin da ya gani a wani otel da yake zaune a Ikoyi ya ba shi mamaki, inda ya hango rakiyar tsaro mai yawa da ya ce “ta isa ta kwace ƙasa”. Bayan ya bincika, sai aka tabbatar masa cewa rakiyar ta ɗan shugaban ƙasa ce. Soyinka yace hatta mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya nemi karin bayani kan wannan al’amari, yana mai cewa wannan dabi’a ta nuna amfani da iko fiye da kima.

A cikin jawabin nasa, Soyinka ya jaddada cewa “’ya’yan shugabanni ba zababbun jagorori ba ne, don haka ba su da hurumin amfani da tsaron gwamnati irin na manyan jami’ai.” Ya yi ishara da cewa kasar na fama da hare-haren ‘yan bindiga, sace mutane, da rikice-rikicen karkara, don haka bai dace a tara rundunar tsaro a kan mutum ɗaya ba.

Farfesan ya kuma yi tsokaci kan batutuwan yankin, ciki har da tsoma bakin Najeriya wajen dakile juyin mulki a Jamhuriyar Benin, yana mai cewa hakan na iya janyo barazana ga tsaron cikin gida. Ya yi suka kan rusau a Legas, yana mai cewa ko da gwamnati na yin gyare-gyaren birni, ya kamata a kula da mutuncin jama’ar da abin ya shafa. Haka kuma, ya gargadi manema labarai da su kara taka tsantsan da tantance gaskiya domin kaucewa yada bayanan karya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version