A ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ƙara ƙaimi wajen tallafa wa Najeriya domin magance matsalar tsaro da ke addabar yankin Arewa. Macron ya wallafa saƙon ne a shafin X, yana mai cewa hulɗar ƙasashen su da Najeriya na bukatar ƙarfafawa domin tunkarar ƙalubalen tsaro.

Macron ya ce ya yi magana da Shugaba Bola Tinubu, inda ya tabbatar masa da cewa Faransa za ta ƙarfafa haɗin kan ta da hukumomin Najeriya, musamman wajen taimaka wa al’ummomin da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a arewacin ƙasar. Ya ce bai kamata ƙasashen duniya su tsaya kallon irin wannan rikici ba tare da ɗaukar mataki ba.

Kakaki24 ta tattaro cewa Macron ya kuma yi kira ga ƙasashen abokan Faransa su ƙara zurfafa hulɗa da Najeriya, yana mai jaddada cewa goyon bayan ƙasa ɗaya kaɗai ba zai wadatar ba wajen magance wannan barazana ga zaman lafiyar yankin.

Wannan furuci na Macron na zuwa ne a dai-dai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale kai tsaye hare-haren da ake yi wa mabiya addinin Kirista a Najeriya — zargi da gwamnatin Najeriya ta karyata, tana mai cewa ana ɗaukar dukkan matakan kariya ba tare da nuna bambanci ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version