Rahoton jaridar The Punch ya bayyana cewa sama da manyan hafsoshin soja 500, ciki har da Major-General, Brigadier-General, Rear Admiral da Air Vice Marshal, an tursasa musu yin ritaya daga rundunonin soja tun daga lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari zuwa Bola Tinubu, duk da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar. Wannan al’ada ce da ake kira “military tradition”, wadda ke tilasta manyan jami’an da suka fi sabon hafsan hafsoshin soja girma ko suka yi kwas ɗaya da shi su bar aiki domin kiyaye tsarin girmamawa da ladabi a runduna.
An fara wannan jerin ritaya ne a shekarar 2015, bayan da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya nada sabbin hafsoshin soja, inda sama da janar 100 daga rundunar sojojin ƙasa suka bar aiki. Wannan al’ada ta sake maimaituwa a 2021 da kuma lokacin da Tinubu ya hau mulki a 2023, inda karin janar 51 daga rundunar ƙasa, 49 daga rundunar sama, da kuma 17 daga rundunar ruwa suka yi murabus. Sabuwar nadin hafsoshin soja da Tinubu ya yi makon da ya gabata, na iya sake tilasta karin jami’ai 60 yin ritaya idan aka ci gaba da bin wannan tsari.
Wasu tsofaffin manyan hafsoshi kamar Janar Ishola Williams (rtd.) sun soki wannan tsarin, suna cewa yana kawo cikas ga ci gaban sojoji da tsaro, tare da bayyana shi a matsayin abin da ke kama da tsarin mulkin soja. Sauran tsofaffin hafsoshi sun ce ya kamata gwamnati ta rage yawan janar-janar da ake haɓakawa domin kauce wa irin wannan tarin ritaya, yayin da wasu suka ba da shawarar amfani da gogewarsu a matsayin masu ba da shawara ko hafsoshin ajiya (reserves).
Sai dai wasu, kamar Janar PJO Bojie (rtd.), sun bayyana wannan al’ada a matsayin abu na yau da kullum a rundunar soja, suna mai cewa yana taimakawa wajen sabunta tsarin aiki da inganta ladabi. Duk da haka, masana harkar tsaro sun jaddada cewa idan aka ci gaba da barin siyasa ta tsoma baki cikin tsarin soja, to za a ci gaba da fuskantar irin wannan matsala ta yawan janar-janar da ake tursasa musu barin aiki duk lokacin da aka nada sabbin hafsoshin runduna.
