Farashin gas din girki ya ƙaru sosai a sassan Najeriya, inda kilo ɗaya kai har ₦2,000 zuwa ₦3,000 a wasu wurare. Sai dai Ƙungiyar Masu Sayar da Gas ta Najeriya (NALPGAM) ta bayyana cewa wannan tashin farashin bai da alaƙa da wani hukuncin gwamnati, illa dai matsalar isar da kayayyaki da kuma cin moriyar kasuwa da wasu ‘yan kasuwa ke yi.
Shugaban ƙungiyar, Oladapo Olatunbosun, ne ya bayyana hakan yayin hirar sa a gidan talabijin na Channels, inda ya ce babu wani sabon ƙarin farashi daga hukumomi. Ya ce matsalar ta samo asali ne daga tsaikon samar da gas sakamakon gyaran da masana’antar Dangote Refinery ta fara, wanda ya rage fitar manyan motoci masu ɗaukar gas daga yard ɗinta daga kusan motoci 50 a rana zuwa kaɗan.
Bayan wannan, yajin aikin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) ta yi ya ƙara tsananta matsalar ta hanyar hana sauke jiragen ruwa a tashoshin Apapa, wanda ya haifar da ƙarancin kaya a kasuwa. Wannan ya ba wasu ‘yan kasuwa damar tsoma baki wajen ɗaga farashi ba bisa ƙa’ida ba.
Olatunbosun ya bayyana cewa kafin wannan matsalar, farashin gas a gonakin bottling bai wuce ₦1,000 zuwa ₦1,300 ba a yankin Yamma, amma yanzu wasu suna sayarwa har ₦1,700 zuwa ₦3,000 ga waɗanda ke siya ta hannun dillalai. Ya shawarci jama’a su rika siye kai tsaye daga gidanjen gas don kauce wa ƙarin farashi.
Ya ƙara da cewa wannan ƙarancin kaya “na wucin gadi ne” kuma ana sa ran farashi zai dawo daidai cikin ‘yan kwanaki, bayan da aka fara dawo da jigilar kaya daga tashoshi da masana’antu.
