Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a wani taron manema labarai da aka gudanar a Enugu, babban birnin jihar. Mbah ya ce matakin ya biyo bayan dogon nazari ne da nufin hada kai da gwamnatin tarayya domin ci gaban jihar da yankin Kudu maso Gabas baki ɗaya.

Gwamnan, wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi, da ‘yan majalisar jiha da na tarayya, ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne saboda ya ga a jam’iyyar APC akwai damar yin hadin gwiwa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo ci gaba mai ɗorewa. Ya ce, “Tabbas Shugaba Tinubu abokin tafiya ne, wanda ke da hangen nesa da ƙarfin guiwa wajen yanke matakai masu wahala don inganta gobe.”

Mbah ya bayyana cewa wannan sauyin ba na mutum ɗaya ba ne, illa matakin hadin gwiwa daga shugabannin siyasa a jihar, ciki har da mambobin majalisar tarayya da jiha, shugabannin kananan hukumomi, da masu rike da mukaman siyasa, sama da kashi 80 cikin 100 na shugabannin jam’iyya a jihar. Ya ce matakin zai bai wa mutanen Enugu da Kudu maso Gabas muryar da za a fi saurara a Abuja.

Yayin da yake gode wa PDP bisa goyon baya tun daga lokacin zabe, Mbah ya bayyana cewa duk da irin biyayyar yankin Kudu maso Gabas ga jam’iyyar, sau da dama muryar yankin ba ta samun isasshen kulawa. Ya ce yana da kwarin gwiwa cewa wannan sabon mataki zai bude sabon babi na ci gaba da cigiyar hadin kai tsakanin Enugu da gwamnatin tarayya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version