Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance. A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha ranar Juma’a, ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan People’s Democratic Party (PDP).
Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin wasu gwamnoni da fitattun ’yan adawa na komawa APC mai mulki a Najeriya. Matakin ya ƙara janyo muhawara a fagen siyasar ƙasar, musamman ganin yadda ake fassara sauye-sauyen siyasa gabanin 2027.
Har yanzu babu cikakken martani daga shugabannin PDP na ƙasa kan matakin gwamnan. A baya-bayan nan kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki Adamawa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka—matakin da wasu ke gani a matsayin zawarcin siyasa.


