Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Mai magana da yawunsa, Daniel Alabrah, ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba 15 ga Oktoba, sai dai bai bayyana dalilan da suka sa gwamnan ya yanke wannan shawara ba, kuma bai ce ko zai koma jam’iyyar APC mai mulki ko ADC ba.

Bayan sanarwar ficewar gwamnan, dukkan mambobin PDP a majalisar dokokin jihar, kwamishinoni a majalisar zartarwa, da wasu manyan jiga-jigai na jam’iyyar a Bayelsa, suma sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa gwamnan yana ganawa da shugabannin jam’iyyar a jihar, inda Kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Abraham Ingobere, ma yake halarta.

Ficewar ta zo ne awanni kaɗan bayan Gwamna Diri da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan suka halarci taron bude otal ɗin Best Western Plus a Yenagoa. Diri ya taba rike mukamin kwamishina a lokacin Jonathan yana gwamnan jihar, sannan ya zama babban sakatare ga tsohon gwamna Seriake Dickson.

Diri ya fara tafiyarsa ta siyasa ne a PDP, inda ya zama ɗan majalisar wakilai a 2015, sannan Sanata a 2019. A 2020 ne ya zama gwamnan jihar bayan nasarar da ya samu a kotu, kuma an sake zaɓensa a 2023 ƙarƙashin tutar PDP — jam’iyyar da yanzu ya bari bayan shekaru da dama a cikinta.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version