Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya kaddamar da aikin gyara na tsawon kwanaki 10 a babban tashar wutar lantarki ta Gombe, lamarin da ake sa ran zai haifar da tangarda wajen samun wutar lantarki a wasu sassan jihar. A cewar TCN, aikin yana cikin tsarin gyaran rigakafi domin tabbatar da ingantacciyar wuta da kwanciyar tsarin wutar yankin Arewa maso Gabas gaba ɗaya.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Ndidi Mbah, ta bayyana cewa za a gudanar da aikin daga ranar 14 zuwa 24 ga Oktoba, daga ƙarfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a kullum, a tashar wutar Gombe 132/33kV. Aikin zai haɗa da rufe wasu layukan wuta da sauya muhimman kayan kula da kariya a tashar Shongo 33kV Feeder 8.

Don rage tasirin aikin ga jama’a, TCN ta ce za ta mayar da nauyin layin Shongo zuwa Darazo 33kV, yayin da layin Mallam Sidi zai koma Doma 33kV. Haka kuma, Kamfanin Rarraba Wutar Jos zai ci gaba da karɓar wuta yayin lokacin gyaran domin tabbatar da cewa jama’a ba su rasa wuta gaba ɗaya ba.

TCN ta nemi hadin kai da fahimtar jama’a, tana mai jaddada cewa gyaran yana da matuƙar muhimmanci wajen kare tsarin wuta daga lalacewa da kuma tabbatar da dogon lokaci na samun wuta mai inganci. Kamfanin ya ce wannan mataki yana daga cikin hanyoyin da yake amfani da su wajen tabbatar da ci gaba da samar da wutar lantarki mai dorewa a Gombe da kewaye.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version