Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya baiwa ma’aikatan jinya da malaman makaranta 72 gidaje a ƙaramar hukumar Mafa, domin yaba musu bisa jajircewarsu wajen hidima ga al’umma.

Daga cikin waɗanda suka amfana akwai wata ma’aikaciyar jinya ƴar ƙabilar Igbo daga Jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, wadda ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a Mafa ba tare da ta bar garin ba — ko da lokacin matsanancin hare-haren Boko Haram.

Gwamnan ya kuma ɗauki ɗanta, Anthony, aiki a Jami’ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri, tare da miƙa musu gidan da duk kayan cikinsa.

Madam Duaka ta bayyana godiyarta ga gwamnan bisa wannan gagarumar kyauta, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da zama a jihar ko bayan ta yi ritaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version