Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da sabon bashin da yake so ya ciyo da ya kai dala biliyan 2.3, da kuma fitar da takardun bashi na Sukuk na duniya na dala miliyan 500.
Shirin zai taimaka wajen aiwatar da kasafin kuɗi na 2025, biyan tsohon Eurobond na dala biliyan 1.1 da zai ƙare a watan Nuwamba 2025, da kuma gina manyan ayyuka.
Gwamnati za ta nemi tallafi daga Hukumar ICIEC domin rage kuɗin bashi da jawo masu saka jari. Wannan shi ne karo na farko da Najeriya za ta shiga kasuwar kuɗin Musulunci ta duniya.
Sabon bashin na zuwa ne a lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin rufe gibin kasafin kuɗi da kula da yawan bashin ƙasa.
