Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana bakin cikinsa kan mummunan haɗarin mota da ya ritsa da fasinjojin motar Kano Line da ta tashi daga Gombe zuwa Kano, inda mutane 13 suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Misilli, ya fitar, gwamnan ya ce lamarin abin takaici ne kuma babban rashi ga iyalan mamatan da kuma al’umma baki ɗaya. Ya miƙa ta’aziyya ga dangin waɗanda suka mutu tare da addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kuma ba wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

Gwamna Yahaya ya kuma jajanta wa kamfanin Kano Line da Ibrahim Dankwambo Mega Motor Park da ke Gombe, inda motar ta fito, yana mai kiran hukumomin sufuri su sake duba matakan tsaro don kauce wa irin wannan masifa a nan gaba. Ya kuma shawarci direbobi da su rika bin ƙa’idodin hanya da taka-tsantsan musamman a tafiye-tafiyen nesa.

A ƙarshe, gwamnan ya roƙi Allah Ya ba iyalan mamatan haƙuri da juriya, tare da addu’ar samun rahama ga waɗanda suka mutu. Ya ce gwamnatin jihar Gombe na tare da su a wannan lokaci na bakin ciki.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version