Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da fitar da kudi naira biliyan 2.321 domin biyan hakkokin fansho, kudin sallama da tallafin mutuwa ga tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu a fadin jihar.
Wannan rabo na cikin tsarin fansho na haɗin gwiwa (CPS) da kuma tsohon tsarin biyan fansho (DBS). Gwamnatin Kaduna ta ce ta riga ta biya jimillar Naira Biliyan ₦6.678 a shekarar 2025, tare da jimillar naira biliyan ₦13.5bn cikin shekaru biyu na wannan gwamnati mai ci.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar ga manema labarai, ya bayyana cewa kulawa da jin daɗin tsofaffin ma’aikata na daga cikin abubuwan da gwamnati ke ba wa muhimmanci. Ya ce Gwamna Uba Sani ya sha nanata cewa kare mutunci da inganta rayuwar tsofaffin ma’aikata ba kawai wajibi ne na doka ba, har ila yau nauyin ne da gwamnati ke ɗauka da muhimmanci.
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, ya ce sabon rukuni na biyan kudi zai amfanar da tsofaffin ma’aikata 661 da iyalan waɗanda suka rasu a matakan gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi. Ya bayyana cewa naira biliyan ₦1.736 za a biya wa tsofaffin ma’aikata 511 karkashin tsarin CPS, yayin da naira miliyan ₦585 za a biya wa tsofaffin ma’aikata 315 da iyalan mamata karkashin tsarin DBS.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ga waɗanda ke karkashin tsarin CPS, za a tura kudaden su kai tsaye cikin asusun fansho (Retirement Savings Accounts – RSAs) ɗinsu. Amma ga waɗanda ke karkashin tsarin DBS, za a gayyace su nan gaba domin yin tantancewa kafin biyan kuɗaɗen su.
A ƙarshe, gwamnatin jihar ta ce wannan mataki ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kare rayuwar tsofaffin ma’aikata, tabbatar da hakkokinsu, da kuma ƙarfafa amincewar ma’aikatan jihar da gwamnati.
