Shekara guda bayan ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri, babban birnin jihar Borno, dubban mutane da bala’in ya shafa har yanzu ba su samu mafaka ta dindindin ba. Ambaliyar ta faru ne a watan Satumbar 2024 bayan Alou dam ya karye sakamakon ruwan sama mai yawa da kuma sakaci wajen gyarawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raba fiye da mutane 300,000 da matsugunansu.
Maryam Jidda, wata tsohuwa mai shekaru 75, ta rasa gidan da ta gina shekaru 11 da suka wuce bayan ta tsere daga hare-haren Boko Haram. Yanzu haka tana zaune ne da yaranta tara a ɗaki guda tare da makwabciya, ba tare da samun damar sake farfado da sana’ar ta sayar da goro ba. Aisha Ali Adamu, wata bazawara mai yara takwas, ita ma tana rayuwa ne da taimakon al’umma tun bayan da ruwa ya shafe gidanta. Yaran nata sun daina zuwa makaranta tun bara saboda rashin kayan karatu da kudin makaranta — matsalar da ta riga ta zama babbar barazana ga ilimi a Borno inda yara fiye da 700,000 ba sa samun ilimi saboda tashin hankali da talauci.
Yawan mutanen da ke gudun hijira daga rikicin Boko Haram da ISWAP ya kara cunkoson Maiduguri, inda miliyoyi suka nemi mafaka cikin shekaru goma da suka gabata. Duk da kokarin gwamnati na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira da mayar da su garuruwansu, mutane da dama sun ki komawa saboda tsoron hare-haren mayaka — kamar yadda aka gani a Darul Jamal a farkon Satumba, inda akalla mutum 63 suka mutu a wani hari.
A halin yanzu, yawancin wadanda ambaliyar ta shafa suna rayuwa cikin talauci da rashin kulawar gwamnati, ba tare da wurin zama ko damar farfado da rayuwarsu ba — abin da ke jawo ayar tambaya kan shirye-shiryen gwamnati na taimaka musu.
