Aƙalla mutane 4,778 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar kwalara a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024, bisa ga rahoton Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC).

Rahoton ya nuna cewa a shekarar 2020 an yi hasashen cewa mutane 3,513 ne su ka kamu da cutar, inda mutum 95 suka mutu. Sai dai a shekarar 2021 lamarin ya ta’azzara matuƙa, inda aka yi zaton mutane 111,062 suka kamu da cutar, yayin da ta yi sanadin mutuwar mutane 3,604 a jihohi 33 na ƙasar.

Shekarar 2025 ma ta ci gaba da zama cike da ƙalubale. A wannan shekarar kaɗai, sama da mutane 300 ne suka mutu sakamakon kwalara. Ciki har da mutane 179 da gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwarsu cikin mutum 12,052 da ake zargin sun kamu da cutar a watan Satumba.

Haka kuma a jihar Bauchi, mataimakin gwamna Auwal Mohammed Jatau ya tabbatar da mutuwar mutum 58 cikin mutum 258 da ake zargin sabbin kamuwa ne da cutar a ƙananan hukumomi 14 na jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito makonni biyu da suka gabata.

Wannan na faruwa ne duk da tallafin kuɗaɗe masu yawa da Najeriya ta samu daga ƙasashen waje da cibiyoyi. Ciki har da bashin miliyoyin daloli daga Babban Bankin Duniya don samar da ruwa da tsaftar muhalli, da kuma tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya na dala miliyan biyu domin samar da rigakafin kwalara.

Tushen labarin: NCDC, Daily Trust.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version