Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta kammala dukkan shirye-shirye na gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira triliyan 1, wanda shi ne mafi girma a tarihin jihar. A yayin bude Taron Majalisar Zartarwa ta Musamman, Gwamnan ya ce wannan kasafi na kunshe da muhimman tsare-tsare da za su inganta manyan ayyuka, gyaran birane da kuma bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Kano.

Ya bayyana cewa karuwar kasafin na biyo bayan inganta hanyoyin tara kudaden shiga na cikin gida da kuma dakile barna da ɓata-ɓatar kudade. Wannan, a cewarsa, zai baiwa gwamnati damar aiwatar da manyan ayyukan cigaba da suka shafi gidaje, aikin gona, ilimi, lafiya da kuma tallafawa kananan masana’antu domin ƙara samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Yusuf ya ce za a mika kasafin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin yin nazari da amincewa, tare da tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gudanar da mulki cikin gaskiya da kula da dukiyar jama’a yadda ya kamata. Ya kara da cewa idan aka amince da kasafin, zai zama na farko cikin jihohin Arewa da ya kai matakin N1 triliyan, abin da ya nuna sabuwar manufar gwamnatin Kano wajen gina ci gaban zamani.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version