Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, na iya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, in ji mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Josiah Kente. A cewar Kente, wannan mataki zai taimaka wajen samar da cikakken haɗin kai da gwamnatin tarayya domin bunkasa ci gaban jihar, musamman wajen samun ayyukan raya kasa da tallafin ƙasa da ƙasa.

Kente ya bayyana cewa ba neman mulki ko amfani na kashin kai ne ya sa ake kira ga gwamnan da ya shiga APC ba, illa kawai don amfanin jama’ar Taraba. Ya ce gwamnatin Kefas ta nuna bajinta wajen ilimi, kiwon lafiya da gine-gine, amma tana bukatar ƙarin goyon bayan gwamnatin tarayya domin ci gaba da aiwatar da shirinta na “Moving Forward.”

Mai ba da shawarar ya ce haɗin gwiwa da jam’iyyar da ke mulki zai buɗe sabbin hanyoyin ci gaba kamar gina manyan hanyoyi, asibitoci, da inganta tsaro. Ya kuma jaddada cewa lokaci ya yi da ake buƙatar shawarwari masu zurfi da suka wuce bambancin jam’iyyu domin amfanin al’umma baki ɗaya.

Idan Gwamna Kefas ya koma APC, hakan zai kawo babban sauyi a siyasar Taraba, wadda ta kasance sansanin PDP tun 1999. Wannan sauyi, in ji Kente, zai zama wata dama ta sabuwar haɗin kai da cigaban jiha, yayin da ake kira daga masu ruwa da tsaki da matasa su mara wa gwamnan baya a wannan yunkuri.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version