Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu tana shimfiɗa sabon tsarin gina tituna da za su iya ɗorewa tsakanin shekaru 50 zuwa 100, domin kawo ƙarshen matsalar lalacewar hanyoyi a ƙasar. Yayin da yake duba aikin titin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano, Umahi ya ce gwamnati ta koma amfani da sabuwar fasaha ta milling, recycling, da ƙarfafa tituna da kankare, domin tabbatar da tsawon rayuwar hanyoyi da rage kashe kuɗin gyare-gyare.
Umahi ya bayyana cewa sabon tsarin zai maye gurbin tsohon “cut-and-fill” da ke haddasa rashin daɗewar tituna. Ya ce maimakon a zubar da tsohon asphalt, za a yi amfani da shi saboda ya fi ƙarfi bayan shekaru na matsin motoci. Ya kara da cewa gwamnati ta fara canza yawancin manyan hanyoyi zuwa rigid pavement wato titunan kankare, waɗanda za su rage yawan ramuka da lalacewar hanya.
A yayin ziyarar, Umahi ya yaba wa kamfanin Infiouest International Limited wanda ke jagorantar aikin, yana mai cewa aikin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano yanzu ya zama abin koyi a ƙasar. Ya gargadi injiniyoyi da kwangiloli da kada su ci gaba da lalata tsofaffin kayan da har yanzu suna da ƙarfi. A cewarsa, asphalt mai kyau zai iya rayuwa fiye da shekaru 25 idan aka sake sarrafa shi yadda ya dace.
A nasa bangaren, Ƙqramin Ministan Ayyuka, Bello Mohammed Goronyo, ya ce wannan tsari yana nuna yadda shugaba Tinubu ke son gina muhimman hanyoyi masu ɗorewa domin inganta tattalin arziki. Ya ƙara da cewa sabbin hanyoyin za su rage lokacin tafiya, kashe kuɗin gyara, da kuma inganta tsaro da kasuwanci tsakanin Abuja da arewacin ƙasar.
