Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da sakin kudaden da suka kai Naira biliyan 7.9 domin biyan bashin kudaden ritaya (gratuity) na shekaru biyar ga tsoffin ma’aikatan gwamnati na jiha da kananan hukumomi. Sanarwar hakan ta fito ne daga Mamman Mohammed, Darakta Janar na Sashen Yada Labarai da Harkokin Jama’a na Gwamnan, a ranar Alhamis 16 ga Oktoba a Abuja.
Daga cikin adadin, Naira biliyan 5.8 za a bai wa Ma’aikatar Kudi ta jiha domin biyan tsoffin ma’aikatan gwamnati, yayin da Naira biliyan 2.1 kuma aka ware wa Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarautu domin biyan tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi daga Janairu 2020 zuwa Mayu 2025. Gwamna Buni ya kuma umarci a saka tsarin biyan kudaden ritaya cikin jadawalin kudi na wata-wata domin gujewa taruwar bashi a gaba.
Wannan mataki, a cewar gwamnati, zai kawo sauƙi ga tsoffin ma’aikata da suka jima suna jiran hakkokinsu, tare da dawo da mutuncin ma’aikata bayan ritaya. Haka kuma, ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da walwalar ma’aikata da tabbatar da daidaiton lamuran kudi.
Kwamishinonin Kudi da na Kananan Hukumomi sun bayyana wannan mataki a matsayin gagarumin ci gaba na tattalin arziki da zamantakewa, wanda zai tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin biyan hakkokin masu ritaya cikin lokaci kamar yadda gwamnati ta tsara.
