Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya zargi gwamnatin tarayya da nuna wariya ta hanyar hana jiharsa tallafin musamman tun bayan hawansa mulki a 2023, yana mai cewa dalilin hakan shi ne kasancewarsa a jam’iyyar adawa ta PDP. A wata hira da ya yi da DW Hausa, Lawal ya ce wasu jihohi sun samu tallafi mai yawa har sama da Naira biliyan 500, amma Zamfara ba ta samu ko sisi ba baya ga kuɗin rabon da take samu na doka.
Sai dai a gefe guda, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnonin APC bisa tallafin Naira biliyan 8 da aka bayar ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Singer. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da tallafin Naira biliyan 5 daga gwamnatin tarayya, yayin da gwamnonin APC suka ƙara Naira biliyan 3 domin rage raɗaɗin asarar da ‘yan kasuwa suka yi.
Gobarar ta lalata dukiyoyi na biliyoyin naira tare da jefa kusan ‘yan kasuwa 1,000 cikin matsala, yayin da wasu mutane bakwai suka ɓace. Gwamna Yusuf ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, yana mai cewa haɗin kai da gwamnatin tarayya zai taimaka wajen bunƙasa ci gaban Kano da kuma tallafa wa al’ummar jihar.


