Gwamnatin Jihar Enugu ta bayyana shirinta na dakatar da zirga-zirgar keke NAPEP, kananan bas-bas da “yellow bus” daga manyan hanyoyi guda biyar a cikin birnin Enugu, domin fara aiwatar da tsarin Bus Rapid Transit (BRT). Wannan mataki na zuwa ne bayan jama’a sun ki amfani da sabbin BRT din da aka kaddamar watanni da suka wuce.
A taron tattaunawa da kungiyoyin direbobi, Kwamishinan Sufuri, Dr. Obi Ozor, ya bayyana cewa sabbin hanyoyin da za su zama na BRT sun hada da Okpara Avenue zuwa Emene Airport; Ogui Road zuwa Naira Triangle; da New Haven zuwa Zik’s Avenue, ciki har da dukkan hanyar Agbani. Hakan zai sanya gwamnati ta karɓi ragamar sufuri a manyan titunan birnin, sai dai motocin haya za su ci gaba da amfani da su.
A cewar Ozor, tsari ne na sake fasalin sufuri, ba na tauye aikin kowa ba. Ya ce BRT za ta kula da manyan hanyoyi, yellow bus a kananan hanyoyi, yayin da keke NAPEP za su zama na karshe wajen kai fasinjoji. Ya ce gwamnati ta riga ta sayo BRT 200 na CNG, da taxi 4,000 na lantarki da za a hada a ANAMMCO cikin watanni uku. Haka kuma tsarin Ije Card na biyan kudi ta hanyar lantarki za a yada shi zuwa miliyoyin mazauna jihar cikin kwanaki 90.
Kungiyoyin direbobi RTEAN, NURTW da kungiyar masu Keke NAPEP sun nuna goyon baya ga tsarin, sai dai sun bukaci gwamnati ta ba su damar shiga harkar BRT da filayen sufuri. Shugaban Keke NAPEP ya bayyana cewa akwai direbobi 18,000 a jihar kuma ya roki gwamnati ta samar da motocin haya ga wadanda ke son komawa wannan aiki.
