Gwamnatin Jihar Kano ta kudiri aniyar yin aiki kafada da kafada don bunkasa kafafen yada labarai na internet. Inda ta ayyana su a matsayin hanyar yada labarai mafi sauri a wannan zamani.

Hakan ya fito ne daga daraktan babban sashen harkokin yada labarai da sadarwa na gwamnati, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, a yayin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jaridar intanet, wanda cibiyar Kano Online Media Chapel ta shirya.

A yayin jawabin sa ga mahalarta taron, Alhaji Sanusi Bature ya nuna goyen baya ga cibiyar tare da tabbatar da cancantar shugabancinta.

Inda ya yaba da shirya wannan horon na farko da cibiyar ta shirya, yana mai cewa jaridar intanet wata mahimmiyar hanya ce ta sadarwa ga al’umma.

Daraktan ya sanar da bayar da gudunmawar kudi Naira Miliyan 2 biyan bukatun cibiyar.

A bangaren kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya tabbatar da cewa gwamnati tana shirin yin aiki tare da wannan cibiya. Ya ce ma’aikatar harkokin yada labarai za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen cibiyar tare da tabbatar da sahihancin labarai a kafafen yanar gizo.

Tun da farko shugaban cibiyar Kano Online Media Chapel, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya nuna godiya ga halartar jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki. Ya kuma bayyana cewa tun bayan kafa cibiyar, an mayar da hankali wajen rajistar ‘yan jarida domin tsaftace aikin jarida ta intanet, sannan an bude asusu domin inganta ayyukan cibiyar.

Dangambo ya bayyana wasu daga cikin kalubalen da cibiyar ke fuskanta, irin su rashin ofishi da rashin isasshen motocin sufuri.

Duk da wadannan kalubale, shugaban ya tabbatar da kudurin cibiyar na ci gaba da aiki cikin kwarewa, inda ya ce “Zamu ci gaba da watsa sahihan labarai da gaskiya, kuma manufofin mu sun tsaya ne kan gaskiya, rashin nuna bambanci, da hidima ga jama’a.”

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga bangaren jarida, gwamnati, da kwararru domin nazarin sabbin abubuwa a aikin jarida na internet tare da rawar da fasahar zamani ta AI ke takawa wajen sauya yadda ake gudanar da labarai a zamanin da muke ciki.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version