Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta bincike kan matsanancin tabarbarewar tsaro da ya sake kunno kai a sassan Najeriya. Ya yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata 25 a makarantar GGCSS Maga da ke Jihar Kebbi, inda ‘yan bindiga suka kai hari suka kashe mataimakin shugaban makarantar.
Kwankwaso ya kuma nuna bakin ciki kan kisan Brig. Gen. Musa Uba a Jihar Borno, yana mai cewa wannan babban koma baya ne ga yunkurin da sojoji da sauran jami’an tsaro ke yi a yaƙi da ta’addanci. Haka kuma ya nuna damuwa da yawaitar sace-sace da hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara, yana kira ga hukumomi su hanzarta ceto waɗanda ke hannun mahara.
A Kano, ya yi nuni da hare-hare da ke faruwa a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa, inda aka rawaito kashe mutane da kuma sace mata masu juna biyu. Ya jinjina wa Gwamnatin Kano kan ƙarin motoci ga jami’an tsaro, sai dai ya ce har yanzu akwai gibi da ake bukatar cike wa domin kare rayukan al’umma.
Kwankwaso ya kammala da kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙarfafa rundunar soji da kuma rundunar ‘yan sanda domin su sake samun kuzari wajen kare jama’a, tare da dawo da kwarin gwiwar ‘yan ƙasa a harkokin tsaro.


