Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne labaran da ke yawo cewa ‘yan bindiga sun karɓe iko da kananan hukumomi tara daga cikin goma sha shida na jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan harkokin yada labarai, Ibraheem Abdullateef, ya fitar a ranar Litinin 06 ga Oktoba, ya ce wannan labari karya ne da aka kirkira don siyasa.

Abdullateef ya tabbatar cewa babu wata LGA da ‘yan ta’adda suka mamaye, kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta hakan. Ya bayyana cewa duk da wasu matsalolin tsaro da aka samu a wasu sassan arewacin jihar, amma batun yan bindiga sun mamaye jihohin an yi ne da gangan domin ƙirƙiro tsoro a zukatan jama’a. Ya zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yada labaran ƙarya don cimma muradun siyasa.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron al’umma, tare da karfafa hadin gwiwar jami’an tsaro da cibiyoyin tsaron al’umma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version