Gwamnatin Tarayya ta fara kwashe ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran waɗanda suka nuna buƙatar a dawo da su gida, inda ake raka su zuwa kan iyakar ƙasar Armenia domin tabbatar da tsaron lafiyarsu. Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugabar Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata. Ta ce kawo yanzu babu wani ɗan Najeriya da rikicin ya shafa, yayin da jami’an jakadancin Najeriya ke bakin iyakar Iran da Armenia domin karɓar waɗanda ke son a kwaso su.
Ta kuma ce a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da tsaro don fara jigilar mutane ta jirgin sama, amma gwamnatin tarayya na ci gaba da shirye-shirye domin kwaso ‘yan Najeriya da ke yankin. A cewarta, da zarar an buɗe sararin samaniyar, tawagar jami’an gwamnati daga ma’aikatu daban-daban za su fara aikin dawo da su gida.


