Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gayyaci manyan hafsoshin sojin kasar zuwa ofishinsa domin tattaunawa kan karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ake kai wa sansanonin soji a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Taron da ke gudana a ma’aikatar tsaron kasar ya samu halartar babban hafsan tsaron kasa, Janar Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu. Haka kuma akwai babban hafsan sojin sama Air Marshal Sunday Aneke da babban hafsan sojin ruwa Vice Admiral Idi Abass, tare da wakilan Hukumar Lekan Asiri ta Kasa da wasu jami’ai.
Rahotanni sun nuna cewa akalla manyan kwamandoji uku sun rasa rayukansu a hannun ‘yan bindiga a Borno a baya-bayan nan, yayin da dubban sojoji suka mutu a hare-hare daban-daban, tare da sace daruruwan fararen hula. Gabanin fara taron, ministan ya ce sun yanke shawarar sake nazarin dabarun yaki da ‘yan bindiga.


