Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe naira ₦8.4 biliyan domin gina sabuwar kasuwar Sokoto Central Market da ta ƙone a shekarun da suka gabata, a wani mataki na farfaɗo da harkokin kasuwanci a jihar. An amince da kuɗin ne a ranar Alhamis, 12 ga Disamba 2025, yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar.
Kwamishinan Ƙasa da Gine-gine, Nasiru Dantsoho, ya bayyana cewa kwangilar za ta kasance a hannun kamfanoni 38, dukkansu ‘yan kasuwa ne daga cikin al’ummar Sokoto. Gwamna Ahmed Aliyu ya ce wannan aiki wani muhimmin alƙawari ne da ya dauka tun lokacin yaƙin neman zaɓe domin dawo da martabar kasuwar da ita ce cibiyar kasuwanci mafi girma a jihar.
A cewar Bechi Hausa da ke bibiyar cigaban lamarin, majalisar ta kuma amince da tsarin kasafin kuɗi na 2026, wanda aka gina bisa tsarin Medium-Term Expenditure Framework, da kuma kwangilar gina sabon ofishin hukumar Alhazai tare da gyaran tsofaffin gine-gine da darajar su ta kai ₦469.1m. Wannan ya nuna abin da gwamnatin Sokoto ke cewa yunƙuri ne na ƙarfafa tattalin arziki da inganta hidimar gwamnati a faɗin jihar.
A baya-bayan nan, gwamnati ta yi gyara a kasafin kuɗin 2025 ba tare da ta taɓa girman kasafin ba, sai dai ta sake rarraba ₦38.81bn zuwa sassa masu muhimmanci domin inganta aiwatar da kasafin yadda ya dace.
