A ranar 11 ga Disamba 2025 kamfanin Dangote Refinery ya sanar da sabon rage farashin man fetur daga N828 zuwa N699, raguwar da ta kai N129 a kowanne lita, kuma saukar farashi na 20 da kamfanin ya yi a bana. Hukumar Petroleumprice.ng ce ta bayyana hakan, tare da tabbatarwar jami’in kamfanin ga jaridar PUNCH.
Dangote ya ce farashin dole ya ci gaba da raguwa yayin da kamfanin ke ƙara samarwa da kuma yin gasa da kayayyakin shigo da waje, inda ya yi nuni da cewa fasa-kwari ya ragu amma bai ƙare gaba ɗaya ba. A cewarsa, burinsu shi ne sayar da man da farashi mai rahusa, ba neman cin gajiya cikin gaggawa ba.
Sakamakon wannan sauyi, wasu manyan rumbunan man ƙasar kamar Sigmund, TechnoOil, AA Rano, NIPCO da Aiteo sun bi sahu wajen rage nasu farashin, alamar yadda kasuwa ke amsa sabon tsarin Dangote.
