A ranar 12 ga Disamba 2025, kotun Abuja da ke Gwarinpa ta umarci a tura tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, zuwa kurkukun Kuje bayan gurfanar da shi kan zargin almundahanar kwangiloli na N2.2 biliyan da EFCC ta gabatar. Ngige ya musanta tuhuma takwas da suka shafi cin hanci da karɓar kyaututtuka daga ‘yan kwangila na NSITF.

Lauyan EFCC ya nemi a tsare shi har zuwa lokacin fara shari’a, yayin da lauyansa ya bukaci a bayar da belinsa saboda dalilan lafiya, yana mai cewa tsohon ministan ya shafe kwanaki uku a hannun EFCC ba tare da cikakkiyar damar kare kansa ba. Haka nan ya ce ana kokarin rage girman hakkinsa na neman beli da kundin tsarin mulki ya tabbatar.

Alkalin kotun, Justice Maryam Hassan, ta dage sauraron bukatar belin zuwa 14 ga Disamba, tare da bada umarni a cigaba da tsare shi a Kuje har sai lokacin da kotun ta yanke hukunci kan belinsa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version