Gwamnatin Kano ta yi kira ga kafafen yada labaran yanar gizo da su rika taka-tsantsan wajen wallafa duk wani rahoto, musamman kan sha’anin tsaro, domin kare martabar al’ummar jihar. Wannan kira ya fito ne daga Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a yayin taron tattaunawa da aka gudanar ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, a dakin taron Ma’aikatar Yada Labarai da ke Sakatariyar Audu Bako, Kano.
Waiya ya ce akwai bukatar ’yan jarida na intanet su dinga zurfin nazari kafin wallafa labarai masu nasaba da tsaro, domin yaɗa bayanan da ba su da inganci kan iya haifar da tashin hankali ko ƙarin matsaloli a jihar. Ya tuna da yadda wata kafar yanar gizo ta wallafa labarin karya kan cewa Kano cike take da ’yan ta’adda, yana mai cewa irin hakan ba kawai ya saba ƙa’idoji ba, har ma yana cutar da zaman lafiyar mutane.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati na ganin irin goyon bayan da kafafen labarai ke bayarwa — ciki har da rahotannin Bechi Hausa — wajen faɗakar da jama’a da kawar da jita-jita. Ya ce wannan haɗin kan ne zai taimaka wajen dakile matsalar tsaro, tare da tabbatar da cewa rahotanni suna fita cikin kwarewa da gaskiya.
A nasa bangaren, shugaban Kano Online Media Chapel, Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya yi alkawarin cewa mambobinsu za su cigaba da aiki da doka, tare da kaucewa rubuce-rubucen da ka iya tada jijiyoyin wuya. Ya ce kafafen yanar gizo suna da rawar gani wajen samar da zaman lafiya, inda mambobin kungiyar suka yaba da wannan taro da ya basu damar fahimtar irin rawar da ya kamata su taka wajen tsaron jihar.
